Comisshinan gudanarwa na Hukumar Alhazai ta Najeria, Olanrewaju ya zanta da Alhazan, yai musu fatan ibada karbabbiya

Hotuna na ziyarar Comisshinan gudanarwa na Hukumar Alhazai ta Najeria (NAHCON), Prince Anofiu Olanrewaju a mazaunar Alhazan Najeria a Muna

Rahoto daga Fatima Dayyab

Comisshinan gudanarwa na Hukumar Alhazai ta Najeria (NAHCON), Prince Anofiu Olanrewaju ya zanta da alhazai yan jihohin Osun, Ogun, Ekiti, Lagas, Oyo, Kwara da kuma jami’an zagaye.

A yayin da Commishinan ya Kai ziyarar, yai fatan alhazan sunyi ibadan aikin Hajji karbabbiya wacce Allah kadai ne zai iya basu ladan da Aljanna.

Yayi fatan alhazan sunyi wa kawunan su addua, iyalan su, yan uwansu, kasar su, jahohin su da Kuma kasar su Najeria gaba daya.

Olanrewaju yai wa alhazan murnar babbar sallah a kasar mai tsarki.

Ya tunatar dasu da cewa an kusa fara jigilar su dawowa Nigeria, tare da tunatar dasu akan bin dokar tsarin nauyi kilogram 32 na jakakkuna da kuma kilogram 8 na akwatunan hannu.

Ya dada tunatar dasu akan cewa ba a barin jakakkunan kaya da suka wuce kima.

Commishinan ya sanar da alhazan cewa karsu suyi jigilar ruwan zamzam saboda Hukumar alhazan, NAHCON ta riga ta kawo musu zamzam mai yawan lita biyar biyar zuwa Najeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here